Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana nazarin yiwuwar kara tsananta hare-haren bama-bamai kan Iran, a daidai lokacin da rikici ke ci gaba da yaduwa a Gabas ta Tsakiya, bayan da Saudiyya ta fara kai hare-hare kan mayakan Houthi na Yemen.

Kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito cewa Trump ya gudanar da wata ganawa da manyan mashawartansa domin tattauna yiwuwar fadada aikin soji a kan Iran. Sai dai shugaban ya shaida wa manema labarai a Fadar White House cewa har yanzu bai yanke hukunci na karshe ba, sannan kuma gwamnatin Amurka na ci gaba da tattaunawa da shugabannin Iran.

Trump ya kuma yi gargadin cewa Iran na da zabi guda biyu: Ko dai ta cimma yarjejeniya da Amurka ko kuma ta fuskanci hare-haren mafi tsanani fiye da na yanzu.

Sai dai daga nata bangare rundunar sojojin juyin juya halin Musulumcin Iran ta yi gargadin kai harin ramuwar gayya a dukkan sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya  tare kuma da yin kira ga fararen hula da su guji duk wuraren da sojojin Amurka ke zaune.