
Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Hoton Epstein da Michael Jackson Bayani kan maƙalaMarubuci, Christal HayesSanya sunan wanda ya rubuta labari,
Sa’a 1 da ta wuce
Lokacin karatu: Minti 7
Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta fitar da kashi na farko na takardun da ke ƙunshe da bayyanai masu alaƙa da Jeffrey Epstein.
Takardun sun haɗa da hotuna da bidiyo da kuma sakamakon bincike, kuma ana tsammanin ganin cikakken bayanai bayan Majalisar dokoki ta amince da dokar da ta tilasta fitar da bayanan kundin baki ɗaya.
Sai dai ƴan jam’iyyun Democrat da Republican sun zargi ma’aikatar shari’a da karya dokar shari’a bayan da ta ce ba za ta iya fitar da dukkan takardun ba a wa’adin da aka ware mata.
Akwai fuskokin shahararrun mutane a kundin da suka haɗa da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da Andrew Mountbatten-Windsor da kuma da mawaƙa irin su Mick Jagger da Michael Jackson.
Ci gaba da karantawa
Sai dai fitowar hoto ko suna a cikin kundin ba alama ba ce ta aikata laifi. Sannan yawancin waɗanda aka gano a cikin kundin lalata na Epstein sun musanta ayyakata laifi.
Bill Clinton na ninƙaya cikin ruwan ɗimi

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Bill Clinton na ninƙaya
Hotunan da dama da aka fitar sun haɗa da na tsohon shugaban Amurka Bill Clinton.
Wani hoto ya nuna shi yana ninƙaya a cikin tafki, wani kuma ya nuna shi kwance kan sa akan hannayensa ta baya cikin wani abin da ake ganin kamar tafkin ruwan ɗimi.
An dauki hotunan Clinton tare da Epstein da dama a shekara ta 1990 da kuma farkon shekara ta 2000, kafin a fara tona asirin attajirin. Wadanda suka tsira daga cin zarafin Epstein ba su zarge shi da aikata laifuka ba, sannan ya musanta aykata laifi.
Wani mai magana da yawun Clinton ya yi ƙarin bayani game da sabbin hotunan, waɗanda ya ce an jima da ɗaukarsu.
“Suna iya sakin tsoffin hotunan da aka ɗauka sama da shekara 20 da suka gabata, amma wannan batu ba zai taɓa shafar Clinton ba, “in ji Angel Ureña.
“Mutane sun kasu kashi biyu a wannan dambarwa. Rukunin farko ba su san komai game da lamarin ba kuma sun daina mu’amala da Epstein tun kafin a bankaɗo laifukansa. Kashi na biyu kuma sun ci gaba da alaƙa da shi.
“Muna cikin rukunin farko, babu wata matsin lamba daga rukuni na biyu da za ta sanya mu sauya matsaya.
“Kowa, musamman MAGA, na da abin faɗa.”

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Clinton na hutawa cikin ruwan ɗimi.
Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Bill clinton tare da Jeffrey Epstein sanye da rigunan siliki suna kallon kamera.
Zargin yadda Epstein ya gabatar wa da Trump ƴar shekara 14
Har ila yau, an ambaci shugaban Amurka a cikin kundin bayanan da ma’aikatar shari’a ta fitar.
Takardun kotu sun yi cikakken bayani game da zargin Epstein da gabatar da wata yarinya ƴar shekara 14 ga Trump a wurin shaƙatawa na Mar-a-Lago da ke Florida.
Yayin ganawar da ake zargin a 1990, Epstein ya zunguri Trump “cikin wasa ya tambaye shi”, game da yarinyar, “ko ka gamsu?”, kamar yadda bayanan cikin takardun suka nuna.
Takardar ta ce “duk sun yi dariya” amma yarinyar ta nuna ba ta ji daɗi ba, “amma a lokacin ta yi ƙanƙanta ta fahimci abin da suke nufi”.
Yarinya ta yi zargin cewa Epstein ya kula da ita sannan ya ci zarafinta na shekaru da dama.
Amma a kotu ba ta zargi Trump da aikata laifin komai ba.
BBC ta tuntubi fadar White House domin jin ta bakinta.
Lamarin da ake zargin yana ɗaya daga cikin abubuwan da shugaban ƙasar ya ambata a cikin kudin da aka fitar ranar Juma’a, inda a ciki ana iya ganinsa a hotuna da yawa.
An wallafa hoton Clinton a shafin Trump na sada zumunta X , bayan fitar kundin.
Har ila yau, sakatariyar yaɗa labaran Trump ta sake wallafa hotunan Clinton, tana mai cewa “Oh ni ƴa su!”
Duk da haka, akwai sauran shafukan da za a saki.
Mataimakin babban lauyan gwamnati Todd Blanche ya ce ana ci gaba da duba shafukan “dubun dubata” kafin a sake su.
A baya dai shugaban na Amurka ya ce shi abokin Epstein ne na tsawon shekaru, amma ya ce sun rabu a kusan shekara ta 2004 kafin a kama Epstein.
Trump ya sha musanta duk wani laifi da ya danganta shi da Epstein.
Hoto ya nuna Andrew kwance kan cinyoyi

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Tsohon hoton Andrew kwance a kan cinyoyin mata
Wani hoto daga cikin kundin da aka fitar ya nuna Andrew Mountbatten-Windsor yana kwance a kan mutane biyar, waɗanda aka ɓoye fuskokinsu.
An ga abokiyar laifin Epstein, Ghislaine Maxwell a cikin hoton tana tsaye a bayansu.
Andrew ya fuskanci binciken shekaru da dama game da alaƙarsa da Epstein, wanda bai bayyana a hoton ba.
Ya sha musanta aikata laifukan da suke da alaƙa da Epstein, ya kuma ce bai “ga wata shaida ko wata mu’amala da ta haifar da kama shi da kuma yanke masa hukunci ba”.
Michael Jackson da Diana Ross da Chris Tucker da kuma Mick Jagger
Sabbin takardun da aka fitar sun ƙunshi fitattun taurari a cikin kundin lalatar na Epstein.
Attajirin na da alaƙa da taurari da ƴan siyasa da kuma ƴan kasuwa.
Wasu hotuna da ma’aikatar shari’a ta fitar sun nuna shi da taurari da suka hada da Michael Jackson da Mick Jagger da kuma Diana Ross.
Ba a gano wuri ko lokacin da aka ɗauki ɗaya daga cikin hotunan ba, amma babu tabbas ko Epstein yana da alaƙa da dukkansu ko kuma ya halarci waɗannan wuraren. Hotunan da aka fitar a baya daga gidan Epstein sun haɗa da hotunan da ba shi ya ɗauka ba da kuma bukukuwan da bai halarta.

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Mick Jagger tare da Clinton
Wani hoton Jackson ya nuna shi tare da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da Diana Ross. Suna fitowa tare daga wani ɓangare yayin da aka ɓoye fuskoki a hoton.
Wani hoto a cikin kundin ya nuna fitaccen jarumin nan na Rolling Stones Jagger yana daukar hoto tare da Clinton da wata mata da aka ɓoye fuskarta.
Hotuna da dama sun haɗa da jarumi Chris Tucker. Ɗayan ya nuna shi kusa da Clinton a teburin cin abinci. Wani kuma ya nuna shi a filin jirgin sama tare da Ghislaine Maxwell, wanda aka yankewa hukunci.
BBC ta tuntubi Jagger da Tucker da kuma Ross don ƙarin bayani. A baya Clinton ya musanta sanin batun Epstein na lalata amma kuma mai magana da yawunsa a ranar Juma’a ya ce hotuna ne na shekarun da suka gabata.
“Wannan ba shi da alaƙa da Bill Clinton, ba zai taɓa aikata haka ba,” in ji kakakin sa.

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, An ɗauki hoton Michael Jackson da Diana Ross tare da Clinton 
Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Chris Tucker tare da Ghislaine Maxwell abokiyar hulɗar Epstein
Maxwell a fadar gwamnatin Birtaniya
Cikin hotunan da aka fitar ranar Juma’a akwai wani da ya nuna Ghislaine Maxwell a fadar gwamnatin Birtaniya.
Tana tsaye ita kaɗai, sai dai ba a bayyana abin da ya kai ta ba.
Kuma ba a iya tantance wane ne firaminista a lokacin da aka ɗauki hoton ba.

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Babu bayanin abin da Maxwell ta je yi a fadar gwamnatin
Yadda Epstein ya yi barazanar ƙone gida, in ji wata mai zargi
Maria Farmer, wadda ta yi aiki da Epstein, ta shaida wa hukumar bincike ta FBI a cikin rahoton shekara ta 1996 cewa ya saci wasu hotunan sirri da ta ɗauka na ƴan uwanta masu shekara 12 da 16.
A cikin ƙorafin ta ce ta yi imanin ya sayar da hotunan ne ga masu son saye, kuma ta ce ya yi barazanar ƙona gidanta idan ta tona masa asiri.
An ɓoye sunanta a cikin kundin amma Farmer ta tabbatar bayanan ta ne.
Akwai dubban shafuka da ba a fitar ba
Daga cikin takardun da aka fitar ranar Juma’a akwai da dama waɗanda aka yi wa gyara, ciki har da bayanan ƴan sanda da rohoton sakamakon bincike da kuma hotuna.
Fiye da shafuka 100 a cikin kundin masu alaƙa da binciken shari’a aka shafe.

Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, Sama da shafuka 100 aka shafe a kundin
Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, An shafe wasu bayanan da baƙin fenti don ɓoye adireshi da lambobi da sauransu
Asalin hoton, US Department of Justice
Bayanan hoto, A nan babu bayanin da aka ɓoye duk da cewar akwai adireshin Epstein
Dubban shafukan da aka fitar a ranar Juma’a tsakure ne na abin da ke tafe, a cewar ma’aikatar shari’a.
Mataimakin babban mai shari’a Todd Blanche ya sanar da cewar ma’aikatar za ta fitar da “dubban shafuka” a ranar Juma’a kuma yana sa ran za a sake sakin “dubun dubata” a makonni masu zuwa.
Ya faɗa wa Fox & Friends cewa sashen yana bincikar kowane shafi na kundin don tabbatar da cewar an kare ”suna da bayanan duk waɗanda aka ci zarafinsu “. Ya ce wannan tsarin zai ɗauki lokaci.
Ba a sanar da lokacin da za a saki sauran bayanan ba, ƴan majalisa daga kowanne ɓangare sun bayyana rajin jin daɗinsu.
Ƴan jam’iyyar Democrats da suka haɗa da Ro Khanna sun yi barazanar ɗaukar mataki kan membobin ma’aikatar shari’a da suka haɗa da tsigewa ko shigar da ƙara akan ɗaukar lokacin mai tsawo.
Khanna tare da ɗan majalisa daga jam’iyyar Republican Thomas Massie sun jagoranci kaɗa wata ƙuri’a kan kundin lalatar na Epstein inda suka yi watsi da buƙatar shugaban Amurka Donald Trump wanda da farko ya nemi jam’iyyarsa ta juyawa yunƙurin baya.