Firaministan Burtaniya Andy Burnham ya shaida wa majalisar dokoki cewa akwai alamu masu karfi da suka nuna Iran na da hannu a yunkurin kai hari sansanin sojin sama na Fairford da ke Burtaniya.

Fargabar harin ta sa aka janye jiragen manyan jiragen yakin Amurka samfurin B-2 daga sansanin

Lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar 27 ga watan Satumba lokacin da aka kama wasu matasan sojin Burtaniya su biyar ‘yan shekaru 20 da haihuwa a kusa da sansanin bisa zargin ta’addanci da nakiyoyi. Daga baya an sake su a matsayin beli ba tare da wata tuhuma ba.

A makon da ya gabata shugaban Amurka Donald Trump ya baiyana cewa wata barazana da aka danganta da Iran, ta sanya dauke jiragen Amurka masu luguden bama bamai daga sansanin. Bugu da kari Jami’an Amurka sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa ana zargin wata makarkashiyar kai hari da Iran ke shiryawa ta amfani da jirgi mara matuki.

Iran din ta musanta hannu a yunkurin hari a sansanin sojin sama na Fairford a Burtaniya kamar yadda kafofin yada labarai kasar suka sanar.