Wannan ce bayyanarsa ta farko a gaban kotu, bayan garkuwa da shi a birnin Caracas a wani farmakin da dakarun Amurka suka kai a ranar hudu ga watan Janairun 2026, wanda ya share fagen shirin Washington na mamaye kasar mai arzikin man fetur.
Maduro mai shekaru 63a duniya, na fuskantar tuhumar safarar miyagun kwayoyi tare da matarsa Cilia Flores. A yanzu haka ana sa ido kan mataki da martanin da Venezuela za ta mayar, bayan da mataimakiyar Maduro da aka amince ta fara mulkin rikon kwarya Delcy Rodriguez,ta lashe amanta kan mika wuya da bukatun Trump, tana mai cewa har yanzu Maduro ne shugaban kasa.
Shugaba Trump ya sanar da cewa ita ce ke jagorantar al’ummar Kudancin Amurka, sai dai babu tabbas kan zahirin yadda hakan zai tabbata.